Babbar Kotun Jihar Kano dake zamanta a Bompai karkashin jagorancin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya akan wani matashi mai suna Abdulaziz Umar mazaunin Unguwar Fagge a Jihar Kano bayan samun sa laifin kashe Mubarak Salisu lokacin da suke korarin karbe masa waya aka titin race course dake Nassarawa GRA.
Yayn yanke hukuncin a ranar litinin din data gabata Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta tabbatar da cewa lauyar gwamnati ta tabbatar da shari’arsa ba tare da wani shakku ba.
Kotun dai ta tuhumi Abdulaziz Umar da wasu abokansa hudu Umar Sarki, Diga, Ashosho, da Taduke wadanda dukkanin su suka cika rigar su da iska har yanzu ba’a kai ga kamasu ba.
Lauyar gwamnati, Aisha Salisu ta gabatar da shaidu hudu da suka bada shaida a kan wanda ake tuhuma, yayin da lauyan wanda ake tuhuma, Ya’u Abdullahi Umar, ya gabatar da wanda ake tuhuma shi kadai a matsayin shaida sakamakon guduwar da sauran wadanda ake zargi.
Tun da farko kotun ta tuhumi Abdulaziz Umar da wadanda ake nema sun hada baki don aikata laifin kwace waya kirar Samsung mallakar Mubarak Salisu (wanda aka kashe) wadda darajarta ta kai N100,000.00, kuma sun aikata wannan laifi bisa yarjejeniyar da ta sabawa Sashe na 97 na kudin laifuka,Penal Code ta Kano 1990 wadda aka gyara.
Sai kuma tuhuma ta biyu dake cewa wadanda ake zargin sun yi amfani da wuka mai kaifi, inda suka yiwa Mubarak Salisu (wanda aka kashe) sata waya kirar Samsung wadda kudin ta yakai N100,000.00, wanda ya sabawa Sashe na 298 na dokar kundin laifuka ta Kano 1990, kamar yadda aka gyara.
Tuhuma ta uku tace wadanda ake zargin sun aikata laifin kisan kai akan Mubarak Salisu ta hanyar caka masa wuka a ciki da hannu da sanin cewa mutuwa zai mutu, wanda ya sabawa Sashe na 221 na Dokar Penal Code ta Kano 1990, Cap. 105 (kamar yadda aka gyara).
Cikin tuhuma ta hudu kotun ta zargi mutanen biyar da laifin aikata ta’addanci wanda sanadin mutuwar wanda aka yiwa, Mubarak Salisu karkashin jagorancin Abdulaziz Umar ranar 1 ga Oktoba, 2020 a Titin Race Course wanda ya sabawa Sashe na 302 na Dokar Penal Code ta Kano 1990, Cap. 105 (kamar yadda aka gyara).

