Assault

Kisan Sheikh Masussuka: Kungiyar Ansaru Ta Dauki Alhaki – Barista Bulama Bukarti

images (8)
images (8)

Kungiyar mayaka ta Ansaru wadda ke alaka da kungiyar Al-Qaeda ta dauki alhakin kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke Dutsin-Ma, Jihar Katsina.

Crime Detail ta rawaito cewa wannan na cikin rahoton da Jaridar Daily Nigerian ta wallafa, Wanda tace  mai sharhi kan al’amuran tsaro, Barista Audu Bulama Bukarti ya wallafa.

Acewar masanin tsaron kungiyar ta tabbatar da daukar alhakin kisan malamin ne Wanda rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa ya rasu a asibi sakamakon harbin bindigar da mahara suka yi masa a gidan sa, cikin sakon muryar da Barista Bulama Bukarti yace kungiyar ta saki  a ranar Talata, tana Mai zargin marigayin da furta kalaman da suka kafirta shi.

Ansaru ta ce ta kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare, duk da cewa ta ambaci ranar Talata a matsayin ranar da lamarin ya faru, bayan rahotanni sun tabbatar da faruwar labarin a ranar Litinin.

Ƙungiyar ta zargi Sheikh Masussuka yin fito na fito da koyarwar Musulunci.

Barista Audu Bulama Bukarti yace an kashe Sheikh Masussuka yayin da yake tsaka da kokarin assass wani taro da ka iya zama silar wanzar da zaman lafiya tsakanin mutane, labarin da wasu ke ganin na iya zama musabbabin yi masa kisan gilla

Ansaru dai ta sha daukar alhakin kisan Kai a lokuta da dama, tun bayan da ta yiwa kungiyar Boko Haram tawaye.

 

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *