Uncategorized

Adamawa: ‘Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kisan Kai

f539bfaf 63c0 4a95 8a6f e36614955311
f539bfaf 63c0 4a95 8a6f e36614955311

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta sanar da kama wani mutum mai suna James Gambo, bisa zarginsa da hannu a kisan Faisal Usman a yankin Wuro Jibril da ke Karamar Hukumar Mubi ta Kudu. Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Oktoba, 2026, bayan da ake zargin James Gambo ya samu sabani da Faisal Usman, inda ake zargin ya daba masa wuka a wuya, lamarin da ya jikkata shi sosai.

Crime Detail ta rawaito cewa wannan na kunshe cikin sanarwar da rundunar ta fitar inda tace jami’an ’yan sanda sun gaggauta isa wurin, inda suka dauki Faisal Usman zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa. Sai dai duk da kokarin da aka yi na ceto rayuwarsa, ya rasu yayin da yake karbar magani.

Daga bisani jami’an tsaro suka kama wanda ake zargin, kuma a halin yanzu yana tsare yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa, CP Kabir Umar Hassan ya yi Allah-wadai da duk wani nau’in tashin hankali, tare da kira ga al’umma da su rika warware rikice-rikice cikin lumana, maimakon daukar doka a hannunsu.

Ya kuma tabbatar wa iyalan marigayin da jama’a cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru, sannan a gurfanar da duk wanda aka tabbatar da hannu a lamarin a gaban shari’a.

CP Kabir ya kuma umarci sashin binciken manyan laifuka na Jihar (SCID) da ya karbi ragamar binciken domin gudanar da bincike mai zurfi da sirri, yayin da rundunar ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da taimakawa jami’an tsaro da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano gaskiyar lamarin.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *