HAUSA

EFCC ta Gurfanar ta Wani Mutum kan Zargin Damfarar Sama da Naira Miliyan 13 a  Maiduguri

EFCC Logo
EFCC Logo

 

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati ta Ƙasa (EFCC),shiyyar  Maiduguri, ta gurfanar da wani mutum mai suna Gambo Mohammed a gaban mai Shari’a Babagana Shettima na babbar Kotun Jihar Borno da ke zamanta  a Maiduguri a ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026.

An gurfanar da wanda ake tuhumar ne kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka hada da almundahanar kuɗi da karkatar da kuɗaɗe har Naira miliyan 13,650,000.

Ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen ya ce, Gambo Mohammed, wanda aka fi sani da Modu Gambo, a shekarar 2025 ya karɓi kuɗi Naira miliyan 13,650,000 daga hannun Umar Abubakar da sunan sayar masa da filaye guda biyu da ke yankin Dubai Musari, a ƙaramar hukumar Jere ta Jihar Borno, alhali ya san cewa bayanin ƙarya ne.

Ana zarginsa da aikata laifin da ya saɓa da Sashe na 1(a) na dokar zamba da sauran laifukan damfara ta shekarar 2006, wanda kuma Sashe na 1(3) na dokar ya tanadi hukunci a kansa.

Da aka karanta masa tuhume-tuhumen, wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan.

Lauyan masu gabatar da ƙara, A.D. Abdulmalik, ya roƙi kotu da ta sanya ranar fara shari’a tare da bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Mai Shari’a Babagana Shettima ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Yuli, na shekarar 2026 domin gabatar da shari’a kafin fara sauraro, sannan ya ba da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Maiduguri.

Binciken EFCC ya nuna cewa wanda ake zargin ya karɓi kuɗin ne da nufin sayar da filaye guda biyu da ke kusa da Barikin sojoji na Maimalari a ƙaramar hukumar Jere, amma daga bisani ya karkatar da kuɗin zuwa amfanin kansa.

 

 

Source : EFCC

 

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *