Kotun majistire mai lamba 53 dake zaman ta a Normansland karkashin jagorancin mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti, ta bada belin uku daga cikin matasan nan da aka hango su a fefan bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta da zargin cin mutuncin fitattacan malaman addinin musulmci Sheik Umar Sani Fagge.
Matasan da ‘yan sanda suka gurfanar a gaban kotun sun hadar da Adamu Adamu da Salihu Bala da kuma Hassan Umar bisa zarginsu da Hadai Kai cin zarafi da Kuma yinkurin tayar da tarzoma.
Takardar tuhumar yan sandan ta bayyana cewa, ana zargin matasan guda uku da laifin cin mutuncin sheik Umar Sani Fagge tare da yada wa a kafafan sada zumunta.
Har yau takardar yan sandan ta kara da cewa, akwai wani mutum mai suna Isyaku Mai Fanti da ake neman sa ruwa ajallo bisa zarginsa da hannu kan wannan lamari.
Sai dai bayan karanta musu kunshin tuhme tuhuman da ake yi musu ne, nan take dukkanin matasan guda biyu sun musanta zargin da ake yi musu.
Daga bisani mai shari’a Mustapha Sa’ad Datti ya bayar da belin wadanda ake zargin kan kudi naira dubu hamis hamis ko wannan su, tare da tsayuwar ma’aikacin gwamnatin Kano da ya kai matsayin darakta kuma sai ya samu sahalewa daga ma’aikatar da yake aiki kokuma wani wani malamin jami’a na gwamnatin Kano wanda shima sai ya samu sahalewa daga wurin aikin nasa.
Kotun ta sanya ranar 28 ga wannan watan domin ci gaba da sauraron shari’ar.

