Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), shiyyar Kano ta gano tare da fara rushe wasu koguna da hanyoyin karkashin ƙasa da ake amfani da su wajen shan da fataucin miyagun ƙwayoyi a yankin Rimin Kebe dake karamar hukumar Ungogo.
Tun fari dai jami’an hukumar sun gudanar da wani samame ne a ƙarƙashin shirin “Operation Sharar Mafaka” a yammacin ranar Litinin, 4 ga Mayu, 2026, inda suka kewaye yankin da aka dade ana zargin sa da zama mafakar masu aikata laifuka.
Da isarsu, jami’an sun tabbatar da wanzuwar koguna da dama da masu safarar ƙwayoyi suka gina tare da gyara su domin zama wuraren zama da kuma gudanar da harkokinsu.
An gano cewa wasu daga cikin kogunan sun kasance kamar dakuna da falaye, inda aka tanadi tabarma, matasai, tukwane, kwanuka da sauran kayan abinci—abin da ke nuna ana zaune a wuraren na tsawon lokaci ana kuma gudanar da harkoki akai-akai. Bugu da kari NDLEA ta gano wasu sabbin koguna da hanyoyin karkashin ƙasa da ake ci gaba da ginawa, waɗanda ake zargin za su haɗa wurare daban-daban.
Jami’an sun rushe wasu daga cikin koguna da hanyoyin, yayin da ake shirye-shiryen rusa sauran da kuma tabbatar da tsaro a yankin gaba ɗaya. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin da hukumar ke ƙara kaimi wajen kawar da miyagun ƙwayoyi a jihar Kano.
Kwamandan hukumar na Kano CN DY Lawal ya bayyana cewa, “Za mu ci gaba da bibiyar waɗannan bata-gari ko ina suka buya. Mun kuduri aniyar kawar da fataucin miyagun ƙwayoyi a Kano baki ɗaya. Duk wanda ke cikin wannan haramtacciyar sana’a ya dace ya fice yanzu.”
Ya ƙara da cewa ana gudanar da wannan aiki ne bisa umarnin Shugaban NDLEA, na kasa Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), domin fatattakar masu safarar miyagun ƙwayoyi a ko’ina a Najeriya.
Hukumar NDLEA ta Kano ta kuma yi kira ga al’umma da su rika kai rahoton duk wani abin da suke da shakku akan sa ga ofisoshin hukumar mafi kusa, domin haɗin kai da jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen dakile yaduwar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a jihar Kano.

