EFCC ta Gurfanar ta Wani Mutum kan Zargin Damfarar Sama da Naira Miliyan 13 a Maiduguri
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati ta Ƙasa (EFCC),shiyyar Maiduguri, ta gurfanar da wani mutum mai suna Gambo Mohammed a gaban mai Shari’a Babagana Shettima na babbar Kotun Jihar Borno da ke zamanta a Maiduguri a ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026. An gurfanar da wanda ake tuhumar ne kan tuhume-tuhume
