HAUSA

Tsanyawa: An Bude Ofishin Kano State Neighborhood Watch

 

Map of Tsanyawa 703102, Kano

 

Karamar Hukumar Tsanyawa ta buɗe sabon ofishin rundunar tsaro, ta Kano State Neighborhood Watch, domin ƙarfafa tsaro da rage aikata laifuka a yankin.
Wannan na cikin sanarwar da jami’in tsare-tsaren Shugaban karamar hukumar, Abubakar Mai Daraja Yan’awaki, ya fitar.
wadda  ta ce Shugaban karamar hukumar Tsanyawa, Abdullahi Ishaq Yan’awaki, ne ya jagoranci taron buɗe ofishin, tare da halartar jami’an tsaro da ma’aikatan rundunar ta Kano State Neighborhood Watch.
A yayin taron, Abdullahi Ishaq Yan’awaki ya bukaci hukumomin tsaro su bayar da cikakken haɗin kai ga rundunar, domin tabbatar da tsaron al’umma.
Ya kuma yi kira ga matasan da ke aiki a rundunar da suyi  riƙo da gaskiya da amana, wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar karamar hukumar ta Tsanyawa wadda a baya bayannan ke fuskantar matsalar mahara dake kwararowa daga makwaftan jihohi.

Ana sa ran wannan yunkuri zai taimaka wajen dakile ayyukan bata gari da suka addabi yankin da kuma wasu sassa na karamar hukumar Shanono wadda itama ta sha fama da matsalolin tsaron.

Cikin watannin baya bayannan ne gwamnatin Kano ta kaddamar da hukumar tsaro mai suna Kano State Neighborhood Watch domin kawo karshen matsalolin tsaron dake damun wasu sassan jihar musamman kananan hukumomin Tsanyawa da Shanono da ‘yan bindiga suka sha kai hare-hare.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *