HAUSA

An Bayar Da Belin Sheikh Makwarari Akan Kudi Naira Miliyan Ashirin

FB IMG 17689833854902434
FB IMG 17689833854902434

Kotun Majistri da ke zaman ta Kano ta ba da belin Malam Ibrahim Isa Makwarari kan  kudi Naira miliyan 20, bayan gurfanar da shi bisa zargin mallakar takardun filaye na bogi.

Arewa Updates ta rawaito cewa, ana zargin Malam Ibrahim Isa Makwarari da samun takardun fili guda biyu da ake zargin na bogi ne, waɗanda ke ɗauke da sunayen Alƙasim Usman Baba da Audu Danyaro Fagge.

A ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar 2025, kotun majistri ta ba ’yan sanda umarnin binciken ƙorafin da Ma’aikatar Kasa ta Jihar Kano ta shigar kan wani fili da ke kan titin Ahmadu Bello Way a Kano.

A yayin binciken, an samu wanda ake tuhuma da takardun filayen guda biyu da ake zargin na bogi ne, kuma an ce bai gamsar da jami’an tsaro da bayani kan sahihancin takardun ba.

Bayan karanta masa tuhumar, Malam Ibrahim Isa Makwarari ya musanta zargin.

Lauyansa Barista A. T. Shehu ya nemi kotu ta ba da belin sa, yana mai tabbatar da gabatar da mutane sahihai da za su tsaya masa.

A bangaren gwamnati, mai gabatar da ƙara Barista Nura A. Salisu ya ƙalubalanci neman belin, bisa hujjar cewa tun watan Oktoba na shekarar da ta gabata ake neman wanda ake tuhumar, amma ya ki amsa gayyatar ’yan sanda har sai da aka kama shi bayan samun umarnin kotu, tare da roƙon kotu ta sanya tsauraran sharuɗɗa idan za a ba da belin.

Kotun ta ba da belin Malam Ibrahim Isa Makwarari kan Naira miliyan 20, tare da sharadin kawo mutane biyu da za su tsaya masa, inda na farko zai kasance Hakimin karamar hukuma tare da takardar amincewa daga masarauta, na biyu kuma dan kasuwa mai gida a Kano da ke da takardar mallaka, tare da dukkansu su liƙa hotunansu a jikin takardar karɓar beli.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu na shekarar 2026.

Source: Arewa Updates

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *