HAUSA

Kano:Kotu Ta Sallami Matar Da Tsohon Mijin Ta Ya Zarge Ta Da Hadin Baki Don Yi Masa Fashi

court
court

 

Tunda fari dai an gurfanar da Usaina Sani da kuma Khadija Sani wadda itace tsohuwar matar Abubakar Abdullahi bisa zargin hadin baki domin aikata laifi da fashi da makami, bayan karanto musu laifin sun musanta, inda lauyar gwamnati mai gabatar da Kara Barista Zainab B Aliyu ta roki kotu ta basu wata rana domin karbar bayanan lauyoyin gwamnati kotun kuma ta amince ta aike dasu gidan gyaran hali.

A zaman kotun na yau me gabatar da kara ta shaidawa kotun cewar sun karbi bayanan lauyoyin gwamnati inda suka nuna Zainab ba ta da laifi akan  tuhumar don haka take rokon kotu ta sallameta.

Kotun mai lanba 54 karkashin jagorancin mai shari’a Rabi Abdulkadir ta sallameta nan take shi kuma Usaini aka sameshi da laifin Sata.

Tunda fari dai tsohon mijinta wato Abubakar Abdullahi shine ya shigar da korafi bayan da akayi masa fashi da makami inda ya zargi tsohuwar matar tasa da  cewa itace take hada kai da ‘Yan fashin wajen yi asa fashin.

Bayan fitowa daga kotun wakilin mu ya zanta da wadda aka saki inda ta bayyana farin cikinta tare da godiya ga Allah da ya bayyana gaskiyar  abinda ya faru.

Lauyan da ya tsayawa wadanda ake tuhuma ya yabawa ma’aikatar shari’a ta jihar Kano bisa kokarin ganin anyi adalci a cikin binciken da aka gudanar don tabbar da abinda ya faru.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *