Assault

ADAMAWA: AN KAMA JAMI’IN ’YAN SANDA KAN ZARGIN CIN ZARAFIN YARINYA ’YAR SHEKARU 14

FB IMG 1793126539962
FB IMG 1793126539962

Rundunar ’yan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa ta samu rahoton zargin cin zarafin yarinya ’yar shekara 14 a Karamar hukumar Guyuk, inda ake zargin wani jami’in ’yan sanda mai aiki da hannu a lamarin.

Crime Detail ta rawaito cewa wannan na cikin sanarwar da Mai magana yaqun rundunar, Yahaya Nguroje ya fitar, inda yace rundunar ta ce tana kallon zargin da matuƙar muhimmanci, musamman kasancewar lamarin ya shafi ƙaramar yarinya da kuma jami’in da aka ɗora wa alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kwamishinan ’yan sandan jihar ihar Adamawa, CP Kabir Umar Hassan,  ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike cikin ƙwarewa da adalci, domin gano hakikanin abin da ya faru tare da tabbatar da cewa an yi wa kowa adalci bisa tanadin doka.

Rundunar ta jaddada cewa ba za ta yi sakaci da duk wani zargi mai nasaba da cin zarafi ko laifin aikata ba daidai ba ba.

Rundunar ta kuma sake nanata cewa babu wani jami’in ’yan sanda da ya fi ƙarfin doka, inda ta ce duk jami’in da aka samu da laifin aikata laifi ko kuma rashin da’a a bakin aiki, za a ɗauki matakin da ya dace a kansa bisa doka da ƙa’idojin ladabtar da jami’an ’yan sanda. Tace za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani yayin da binciken ke gudana.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *