Amnesty

Borno; Amnesty International Tayi Allah Wadai Da Kisan Matashi a Wurin Maulud

amnesty international
amnesty international

Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan zargin kisan gilla da aka yi wa wani matashi mai shekaru 15 zuwa 16, Umar Muhammad, wanda aka fi sani da Gajiye a yayin taron Maulidi da aka gudanar a Banki, karamar hukumar Bama ta jihar Borno. Rahotanni sun ce wani jami’in ‘yan sanda mai mukamin Superintendent of Police (SP), wanda shi ne DPO na yankin, ya harbe matashin da bindiga har lahira.

Crime Detail ta rawaito cewa wannan na kunshe cikin sanarwar da Amnesty International ta fitar, inda tace shaidu sun bayyana cewa DPO din da tawagarsa sun isa wajen taron Maulidi ne domin korafin hayaniyar da suke cewa tana fitowa daga lasifikar da ake amfani da su wajen bikin. Masu shirya taron sun bi umarnin ‘yan sandan nan take tare da kashe lasifikar.Sai dai jim kadan bayan haka, an ce DPO din ya dawo wurin tare da karin jami’an ‘yan sanda, inda suka kori jama’a daga wajen taron tare da fara harbe-harbe. A yayin wannan rikici ne aka harbi Umar Muhammad, wanda ya mutu nan take.

Amnesty International ta bukaci rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gudanar da bincike cikin gaggawa, mai zaman kansa kuma ba tare da nuna son kai ba, tare da tabbatar da cewa duk jami’an da ke da hannu a lamarin sun fuskanci shari’a ta adalci. Kungiyar ta ce abin da ya faru da Umar Muhammad na kara tona asirin wani yanayi na take hakkin bil’adama da ake zargin yana faruwa, inda wadanda ake zargi da aikata irin wadannan laifuka ke kubuta daga hukunci. Ta kuma yi gargadin cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya, wadda aka kafa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tana fuskantar zargin sauya matsayinta zuwa barazana ga al’umma, sakamakon zarge-zargen take hakkin bil’adama, rashin hukunta masu laifi.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *