HAUSA

Kungiyar Lauyoyin Gwamnatin Kano Zasu Tsunduma Yajin Aiki

IMG 20260310 WA0004
IMG 20260310 WA0004

Lauyoyin gwamnatin jahar kano na ma,aikatar sharia (ministry of justice kano state )sun shirya shiga yajin aikin sai baba ta gani.

Shugaban kungiyar lauyoyin barrister Abdullahi Aminu Shamsu ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Barrister Shamsu ya bayyana cewar sun zartas da shawarar tafiya yajin aikin ne sakamakon rashin biyan su wasu hakkokinsu da gwamnatin ta ki yi.

Ya kuma bayyana cewar suna ta tiri-tiri da shari,u musamman na manyan laifuka da kuma barazana da suke fuskanta daga yan sharia amma duk da haka hakkinsu na lauya baya fita.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewar tun a baya sun zauna da gwamnatin amma har zuwa yanzu hakkokinsu sun gaza fita dan haka suka zartas da shawarar tafiya yajin aikin

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *