
Kwmaishinan Shari`ah na Jihar kano, Barrister Abdulkarim Kabiru Maude, SAN ya halarci taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki, a harkar Shari`ah da harkokin hakkin Dan`adam, wanda Kungiyar Lauyoyi ta kasa a nan kano,reshen Ungogo ta shirya wanda ya gabata a litinin din nan 12/1/2026.
Taron wanda ya gudana a harabar Babbar kotun Jiha a nan kano, mai taken “tabbatar da hakkin dan`adam hadin kai, da kuma kalubalen dake tattare da hakan ya samu halartar, manya manyan baki, a bangaren shari`ah da hakkin dan`adam da nufin tattauna lamarin da yanda yake gudana da kuma nemo, hanyoyin saukakawa tare da warware, matsalolin dake tattare da kare hakkin dan`adam a Nigeria.
A Jawabinsa Kwmaishinan Shari`ah na kano kuma Babban lauyan Gwamnatin kano, Barrister Maude ya jaddada cewar gwamnatin kano zata cigaba da marawa, bangaren shari`ah baya tare da bada gudunmowar data dace wajen tabbatar da sashin ya cigaba da cin gashin kansa, karkashin hadin gwiwar hukumomin gwamnatin, bisa doron dokar aiki ta shekarar 2009.
Da yake jawabi a cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai, mai taimakawa kwamishinan kan harkokin yada labarai, Abubakar Tijjani Ibrahim ya kara da cewar karkashin kulawar kwamishinan Shari`ar na kano, an samu cigaba ta fuskar gabatar da shari`au daban daban a kotunan Jihar kano, tare d atabbatar da dukka wani jinkiri a sha`anin shari`ah an kau da shi.
Hakazalika ya kara da cewa, Gwamnatin kano, karkashin ma`aikatar, bisa Jagorancin gwamnan kano Abba Kabir Yusuf zata cigaba da baiwa bangaren shari`ar kulawa da gudunmowar data dace, da nufin tabbatar da an samu Adalci a kotu na.
A nata bangaren Kungiyar Lauyoyin cibiyar karamar Hukumar Ungogo wadda it ace ta shirya taron ta yabawa gudunmowar kwamishinan shari`ar dangane da gudunmowar da yake baiwa kungiyar wajan cigaba da tabbatar da hakkin dan`adam da walwala ya tabbata a Jihar kano.

