Babbar kotun Jiha a kano karkashin mai shari`ah Zuwairah Yusuf ta wanke, tare da sallamar wata matar Aure mai Suna Fatima Dahiru wadda aka zarga da kashe Kishiyar ta marigayiya Wasila Yusuf.
Fatima dake zaman Aure a Unguwar Farawa, dake yankin karamar Hukumar Kumbotso a nan kano, an gurfanar da ita a kotu ne, da tuhumar aikata kisan kai, laifin daya saba da sashi na 221 na kundin manyan laifuka da hukunce hukuncen su.
A lokacin da take karanta Hukuncin mai shari`ah Zuwairah Yusuf ta bayyana cewar masu gabatar da kara, ko kadan basu iya gamsar da kotun da hujjoji masu masu ma`ana ba, yanda tuhumar zata tabbata akan Fatima Dahiru, dan haka kotun ta sallame ta, tare da wanke ta nan take.
Hakazalika mai shari`ah Zuwairah ta bayyana cewar, hatta shaidun da masu gabatar da kara suka gabatarwa da kotun, ko kadan basu gamsar da kotun da hujjoji akan tuhumar da ake yiwa wannan mata ba.
“ Tace shaidun da aka gabatarwa kotu, karo kawai suke da juna, wanda basu iya bayyana hakikanin abun dake faruwa da kuma hujja mai karfi ba,”
Kazalika ta kara da cewar hatta suma lauyoyin Gwamnati sun gaza kawo shaidun da zasu tabbatar da tuhumar da ake yiwa Fatima Dahiru, tace don haka kotun ba tada wani zabi illa ta sallami wnanan mata..
Lauyan gwamnati, Barrister Lamido Abba Soron Dinki ya shaida cewar lamarin ya faru a ranar 6 ga watan February na shekarar 2019, a unguwar Farawa, inda suka zarge ta da dukan kishiyar ta da wani karfe,inda a karshe ta mutu bayan an kaita Asibiti kuma likitoci suka tabbatar da mutuwar ta, duk da yake wadda ake tuhuma ta musanta tuhumar da ake mata wanda a yau tace ta godewa Allah domin kuwa ya tabbatar da gaskiyar ta.

