Babbar Kotun Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a H.H. Kereng, ta yanke wa wani alƙalin kotun majistare, Mohammad Suleiman Kumo, hukuncin ɗaurin shekara biyu da watanni shida a gidan yari ko zabin tarar Naira 500,000 bisa samunsa da laifin karɓar cin hanci.
An fara gurfanar da Kumo a ranar 3 ga Disamba, 2025, kan tuhume-tuhume uku da suka shafi cin hanci, wanda Hukumar EFCC shiyyar Gombe ta shigar.
Sai dai a ranar 30 ga Disamba, 2025, lauyan wanda ake ƙara, Adamu Bawa, ya gabatar da ƙorafin farko inda ya ƙalubalanci hurumin kotun game da wannan shari’a, yana mai cewa wanda ake tuhumar masanin shari’a ne don haka Kanata ya yi a kai ƙorafinsa gaban ma’aikatar Hukumar Shari’a maimakon kotu.
Lauyan EFCC, A. Aliyu, ya yi watsi da wannan hujja, yana mai cewa Kumo majistare ne ba cikakken jami’in shari’a ba, inda ya dogara da sashe na 318(1) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara). A hukuncin da ya yanke a ranar 17 ga Fabrairu, 2026, Mai shari’a Kereng ya amince da hujjar masu gabatar da ƙara kan batun ikon kotu.
Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya bayyana cewa Kumo, a matsayinsa na alkalin majistare a Kotun ta Pantami, a ranar 6 ga Nuwamba, 2024, ya karɓi naira miliyan ɗaya (N1,000,000) ta asusun bankin Zenith mai lamba 2273938871 na wani magatakarda a kotunsa, Adamu Ahmed, wanda hakan ya saɓa wa dokar yaki da cin hanci da rashawa ta shekarar 2000.
Da farko dai ya musanta laifin, amma a zaman kotun na ranar 5 ga Mayu, 2026, lauyansa ya sanar da kotu cewa wanda yake karewa zai amsa laifin sa bayan sake karanta masa tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Daga nanne kuma lauyan EFCC ya roƙi kotu da ta hukunta shi tare da umartar ya biya tarar naira dubu dari biyar (N500,000) a matsayin diyya ga hukumar, la’akari da lokaci da kuɗin da aka kashe wajen gudanar da shari’ar.
Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyu da watanni shida tare da zabin biyan tarar naira dubu dari biyu da hamsin (N250,000), sannan ta umurce shi da ya biya naira dubu dari biyar (N500,000) a matsayin diyya ga hukumar.
Lamarin ya samo asali ne bayan da ma’aikatar shari’a ta Jihar Gombe ta samu korafe-korafe daga wasu mutane biyu, Abubakar Isa Jauro Kuna da Suleiman Haruna, kan zargin cin hanci da ake yiwa alkalin na majistire Kumo, wanda bayan bincike, an gurfanar da shi a gaban kotu inda daga bisani aka same shi da laifi tare da yanke masa hukunci.

