Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, ya shiga hannu bayan da wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifin almundahanar kudade har Naira biliyan 33.8.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne karkashin mai shari’a James Omotosho naa ranar Alhamis, 7 ga Mayu, 2026 ya yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman hukunci kan tuhume-tuhume guda 12 da suka shafi almundahanar kudade da suka kai Naira biliyan 33.8.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ce ta gurfanar da Mamman bisa zargin almundahanar kudade sama da Naira biliyan 33 da ake zargin an wawure daga kudaden ayyukan samar da wutar lantarki na Mambilla da Zungeru.
A daya daga cikin tuhume-tuhumen, EFCC ta zargi Mamman da hada baki da wasu jami’an ma’aikatarsa da kamfanoni masu zaman kansu wajen karkatar da kudaden gwamnati ta hanyar wasu kamfanoni masu zaman kansu, alhali ya san kudaden sun samo asali ne daga haramtacciyar hanya.
Haka kuma, a wani tuhume-tuhume na daban, an zarge shi da hada baki da wani mai suna Samson Bitrus wajen biyan dala 665,700 ga kamfanin Mohiba Investment Ltd ba tare da amfani da banki ba, lamarin da ya saba wa dokar hana safarar kudaden haram.
Lokacin da aka kira shari’ar domin yanke hukunci, tsohon ministan bai halarci kotun ba. Lauyansa, Mohammed Ahmed, ya shaida wa kotun cewa sun samu sanarwar ranar yanke hukunci, amma duk kokarin tuntubar wanda yake karewa ya ci tura,said ai daga bisani wani abokinsa ne ya sanar da su cewa Mamman ba shi da lafiya.
Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, SAN, ya musanta wannan bayani, yana mai cewa babu wata takardar asibiti da aka gabatar domin tabbatar da rashin lafiyar Mamman. Ya bukaci kotun ta ci gaba da yanke hukunci bisa tanadin dokar ACJA ta shekarar 2015.
Bayan muhawara mai tsawo tsakanin bangarorin biyu, Mai shari’a Omotosho ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda lauyan wanda ake kara ke ta sauya bayanai kan inda Mamman yake.
Daga bisani, kotun ta same shi da laifi a kan dukkan tuhume-tuhume guda 12 da ake masa na halasta kudaden haram.
Sai dai alkalin ya dage yanke hukuncin zaman gidan yari zuwa ranar 13 ga Mayu, 2026 saboda rashin halartar wanda ake kara.
A karshe , lauyan EFCC ya bukaci kotun ta bayar da sammacin kama shi domin hana yiwuwar tserewarsa daga kasa kafin ranar yanke hukunci, wanda kuma kotun ta amince da bukatar.

