Yayin da ake tunkarar bikin ranar ‘Yan sanda ta kasa na 2026 mai taken “Haɗin Kai Da Gina Al’umma”. Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta shirya gudanar da wasu ayyuka na hulɗa da jama’a domin ƙarfafa dangantaka tsakaninta da mutanen gari.
Taken bana yana nuna muhimmancin haɗin kai tsakanin ‘yan sanda da al’umma wajen tabbatar da zaman lafiya da dorewar tsaro.
Kwamishinan ‘Yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori ya ce, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, shirye-shiryen za su fara daga ranar Litinin, 30 ga Maris 2026, da ayyukan tsaftace muhalli, hulɗa da jama’a da kuma bayar da tallafin kiwon lafiya a yankin Dakata dake karamar hukumar Nassarawa.
Daga nan za a ci gaba da wasu shirye-shirye daban-daban domin ƙara fahimtar da jama’a game da ayyukan jami’an da Kuma Kara inganta mu’amala tsakanin ‘yan sanda da jama’a.
Kamar yadda rundunar ta bayyanan jadawalin shirye-shiryen bikin ranar ‘Yan Sanda na Kasar Zai kama Kamar haka:
• Litinin, 30 ga Maris 2026: Tsaftace muhalli a ƙaramar hukumar Fagge, hulɗa da jama’a da kuma bayar da agajin lafiya a Dakata.
• Talata, 31 ga Maris 2026: Tafiyar wayar da kai (walkathon) daga Mandawari zuwa Tal’udu Flyover, shirin kai tsaye na awa guda a gidan rediyon Dala FM Kano, da kuma ziyara zuwa Kotun Tarayya ta jiha.
• Laraba, 1 ga Afrilu 2026: Tattaunawa da ɗalibai da ma’aikatan North-West University, da wasan ƙwallon ƙafa a filin wasa na Sani Abacha Stadium.
• Alhamis, 2 ga Afrilu 2026: Taron tattaunawa da ƙungiyoyin farar hula (CSOs da CLOs), da kuma ziyara zuwa tashoshin mota da kasuwanni a faɗin jihar.
Waɗannan ayyuka za su haɗa da halartar mambobin matan yan sanda (POWA), da kwamitin kyautatta alaka tsakanin yan sandan da al’umma (PCRC), da ƙungiyoyin farar hula, domin nuna ƙudirin haɗin kai da al’umma.
Za a kammala bikin ne a ranar 7 ga Afrilu 2026 a Eagle Square, inda Sufeto Janar na ‘Yan Sanda zai jagoranci manyan baƙi da masu ruwa da tsaki wajen bikin.
Rundunar ‘yan sandan ta jaddada cewa waɗannan shirye-shirye na nuna ƙudirin su na ƙarfafa haɗin kai da gina amincewa da jama’a. Sun kuma bayyana cewa ‘yan sanda da al’umma abokan hulɗa ne wajen ci gaba, kuma za su ci gaba da aiki tare don magance matsalolin tsaro da inganta rayuwar al’umma a jihar Kano.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori ya gode wa al’ummar Kano bisa goyon baya da haɗin kai da suke bayarwa, tare da kira ga shugabannin al’umma da jama’a gaba ɗaya da su fito su halarci wannan biki domin a haɗa kai wajen gina al’umma mai cike da aminci da tsaro.

